Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Mohammad Abdul’aziz yana fadar haka wa kamfanin dillancin labaran “Ain” a jiya Laraba. Ya kuma kara da cewa tattaunawa da fahintar juna tsakanin kungiyoyi daban daban na kasar da kuma tallafin sauran kasashen duniya sune zasu taimakwa wajen dawo da zaman lafiya a kasar Libya.
Tun farkon wannan shekarar ne dai kungiyoyu masu kishin addini a kasar Libya suka fara kai ruwa rana a tsakaninsu a kokarin da ko wannensu ya ke yi na kama madafan iko a kasar. ABNA